Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Rahoton kafar Fars ya yi bayani game da wata majiyar soja da ta samu bayanan harin inda ta bayyana sabbin bayanai game da harin da jiragen yakin sojojin sama na rundunar sojin saman iran suka kai kan sansanin Amurka a Kuwait. A cewar wannan majiyar soja da aka samu bayanai, a cikin wannan harin sama, jiragen yakin F-5 guda biyu na Iran sun kai hari kan kayayyakin more rayuwa na sansanin sojin saman Amurka da ke Kuwait.
Majiyar ta jaddada cewa jiragen yakin biyu, bayan sun ratsawa cikin ingantattun nau'o'in tsarin tsaron sararin samaniyar Amurka sun samu nasarar kai harin sama, tare da dawowa cikin aminci da sauka lafiya a sansanin sojin sama na shida da ke Bushehr.
Your Comment